Daga: Aliyu Wali
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana ranakun 6 ga Afrilu da kuma 7 a matsayin ranakun komawa makaratun Firamare da Sakandare domin cigaba da Karatun Zango na Uku na shekarar 2024/2025.
Gwamnatin ta ce Makaratun kwana na Firamare da na gaba da Firamare masu zaman kansu su koma ranar Lahadi 6 ga watan AFrilun 2005, yayin da na Gwamnati zasu koma ranar Litinin 7 ga watan Afrilun 2025.
Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwar da Mataimaki na musamman ga Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano a kafafen sada zumunta Sharu Ahlan ya rabawa manema labarai a yammacin ranar Juma’a.
- An Ceto Yaran Arewa A Onitsha Da Aka Sato Da Sunan Marayu
- Rikicin Ƙabilanci Ya YI Ajalin Sama Da Mutane 50 A Filato
Sanarwar ta ce kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Gwani Dokta. Ali Haruna Makoda, ya yi gargaɗin ɗaukar mataki mai ƙarfi kan daliban da suka ƙi komawa a waɗanan ranakun.
Dokta. Makoda ya Kuma shawarci dalibai dasu guji komawa makaratun su da kayayyakin da Basu dace irin su Wukake, Reza, ko kwayoyi, Sanan su kasance masu bin dokoki domin samun cigaban ilimin.
Ma’aikatar Ilimin ta jaddada aniyar ta na zagayawa makaratu domin tabbatar da cewa an fara zangon Karatun yadda aka tsara.
Kwamishina Ali Makoda ya Kuma yiwa dalibai da malaman su fatan samun nasara a Sabon zangon na Uku.