Rikicin Ƙabilanci Ya YI Ajalin Sama Da Mutane 50 A Filato

Rahotanni daga jihar Filato na cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos sun kai 52.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa hukumomin yankin Bokkos da ake rikicin ƙabilanci sun tabbatar da alƙaluman.

Wannan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwakin mutane 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don nemo waɗanda ba a gani ba.

Shugaban Ƙungiyar al’adu ta Bokkos Cultural Development Council (BCDC) Vanguard, Farmasum Fuddang, ya shaidawa tashar Talabijin ta Channels cewa an yi jana’izar mutane 31 a ranar Alhamis tare da wasu yara biyar da suka ƙone ƙurmus a ƙauyen Hurti.

Farmasum Fuddang ya ce an kashe wasu mutane 11 a ƙauyen Ruwi, huɗu a ƙauyen Manguna yayin da aka kashe mutum ɗaya a ƙauyen Daffo duka a ƙaramar hukumar ta Bokkos.

Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da hare-haren tare ta kuma yi kira da a kwantar da hankalk saboda a halin yanzu ana ci gaba da ɗaukar matakan tsaro da suka dace da halin da aka tsinci kai.

Kwamishinar yaɗa labarai da sadarwa ta jihar Filato, Misis Joyce Ramnap ta bayyana damuwarta game da sabbin hare-haren a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda