Home » Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Cigaba Da Taimakon Nakasassu 

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Cigaba Da Taimakon Nakasassu 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada Kudirinta na tallafawa masu bukata ta musamman, musamman masu lalurar laka domin inganta rayuwarsu.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin rabon kayan tallafi da kungiyar masu fama da lalurar laka ta baiwa ya’yan kungiyar da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur.

Kwamishina Waiya ya ce yana da muhimmanci a tallafawa masu fama da lalurar laka saboda mawuyacin halin da suke ciki sakamakon lalurar da kuma iyalansu.

Ya ba su tabbacin gwamnatin jihar Kano za ta cigaba da fito da tallafin don ingantawa masu lalurar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin Kano za ta hada hannu da kungiyar domin samar da cibiyar fasahar sanarwa, sannan a sanya musu kayan aikin a koya musu don inganta rayuwarsu.

A wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar yada labarai Sani Abba Yola ya aikowa Kadaura24, ya ce Waiya ya yabawa iyalan wasu lalurar saboda yadda suke tallafawa yan uwansu, sannan ya ba su tabbacin gwamnatin jihar Kano zata cigaba da tallafawa musu don saukaka musu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?