• Home  
  • Gwamnatin Kano Za Ta Dasa Bishiyoyi Dubu 10 A Kowace Karamar Hukuma
- Babban Labari - Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Dasa Bishiyoyi Dubu 10 A Kowace Karamar Hukuma

Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ce gwamnatinsu za ta dasa bishiyoyi dubu 10 a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ce gwamnatinsu za ta dasa bishiyoyi dubu 10 a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Kwamared Aminu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da shirin fara dashen bishiyoyi a fadin kananan hukumomi 44, da aka gudanar a karamar hukumar Tsanyawa.

Ya ce, dasa bishiya sadakace mai saukin aiwatarwa a tsakanin al’umma, saboda haka za a rabawa limamai da Hakimai da Dagataii da masu unguwanni da sauran masu rike da muƙamin gwamnati bishiya guda-guda  su dasa.

Mataimakin gwamnan ya ce, za su sa ido wurin tabbatar da cewa  duk wanda aka bashi bishiya ya kula da ita harta girma.

Ya kuma bayyana dashen bishiyoyin a matsayin wani yunkuri da zai taimaka wajan kare muhalli daga kwararowar hamada da kuma yaki da matsalar dumamar yanayi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai