Home » Gwamnatin Kano Za Ta Gina Wa Ƴan Jarida Wuraren Kwana

Gwamnatin Kano Za Ta Gina Wa Ƴan Jarida Wuraren Kwana

by Halima Djimrao
0 comment

Kwamishinan yaɗa labarai na jahar Kano Baba Halilu Ɗantiye, ya tabbatar da cewa suna shirye-shiryen gina wuraren kwana a  gidajen yaɗa labaran gwamnati domin a sawwaƙa wa masu aikin dare su samu wurin bacci.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne da ya ke ganawa da ƴan Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin da Harkokin Wasan Kwaikwayo reshen jihar ta Kano, RATTAWU, lokacin da suka kai masa ziyara a ofishinsa.

Ɗantiye ya ce wuraren kwanan da za a gina za su magance ƙalubalen da masu aikin dare da masu fara aiki da sassafe ke fuskanta game da komawa gida da kuma zuwa wurin aiki .

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnatin Kano za ta haɗa har da gidajen yaɗa labarai masu zaman kansu wajen bayar da horo da kuma yin bita domin a kyautata aikin a faɗin jihar, sannan ya jinjina wa ƴan ƙungiyar saboda yadda suke bayar da sahihan labarai kuma ya tabbatar musu da cewa zai taimaka musu su gudanar da ayyukansu da kyau kamar yadda ya kamata.

Shugaban Ƙungiyar RATTAWU ta Ma’aikatan Gidajen Rediyo da Talabijin da Harkokin Wasan Kwaikwayo reshen jihar Kano, Babangida Mahmuda Biyamusu, ya ce sun kai masa ziyarar ne domin su taya shi murnar zama kwamishinan yaɗa labarai.

Babangida Mahmuda Biyamusu ya ce ƴan ƙungiyar sun wuce dubu uku a jahar Kano, kuma ya faɗa wa kwamishinan abubuwan da ke ci wa ƙungiyar tuwo a ƙwarya waɗanda ke buƙatar kulawar gwamnati,  daga ciki akwai rashin wurin kwana a ofis, da kuma rashin motoci,  wanda ke hana su gudanar da ayyukansu da kyau kamar yadda ya dace.

Biyamusu ya tabbatar wa kwamishinan cewa ƙungiyarsu a shirye ta ke ta bayar da tata gudunmawa,  kuma ta yaɗa ayyukan da gwamnatin jahar ke gudanarwa.

Wannan bayani baki ɗaya yana ƙunshe ne a cikin sanarwar Ma’aikatar Yaɗa Labaran jahar Kano, wadda Daraktan Sashen ayyuka na musamman, Sani Abba Yola ya rattaba wa hannu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi