Gwamnatin jihar Kano ta ce za a dawo da karɓar Haraji kullum a hannun matuƙa baburan adaidaita sahu a faɗin jihar domin samar da cigaba ta ɓangaren sufuri.
Kwamishinan Ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Injiniya Muhammad Diggol ne ya bayyana haka a wannan makon a helkwatar Hukumar KAROTA.
Kwamishinan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a sabunta rijistar masu adaidaita sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu a faɗin jihar Kano.
Yace za a ɓullo da sabbin tsare-tsare, waɗanda za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin kullum ba tare da an muzguna musu ba duba da yanayin da ake ciki na matsatsin rayuwa.
Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa adaidaita Sahu, don haka dole ne sai kowane matuƙi ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar Kano baki ɗaya.