Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi bayanin dalilin da yasa farashin man fetur ba zai yi kasa ba.
A wani ƙarin hasken da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya yi, ya bayyana dangantakar dake tsakanin matatun man fetur da kuma farashinsa, sannan kuma yace farashin man ya dogara ne kacokan akan kuɗin gangar mai a kasuwannin duniya, sai dai, Ngelale ya bayyana cewa akwai amfani mai tarin yawa ga duk ƙasar da ta mallaki matatun man fetur masu aiki.
Ngelale yace farashin man fetur ba zai yi ƙasa a nan Najeriya ba, ko da kuwa dukkanin matatun man fetur ɗinta guda biyar suna aiki tare da samar da wadataccen man fetur.
Kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale yace ba yawan matatun man fetur ke sa farashin mai ya yi ƙasa ba, ya ce hakan tatsuniya ce kawai domin babu inda hakan ke faruwa a faɗin duniya.
Kakakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa dalilin da ya sanya farashin man fetur ba zai yi ƙasa ba ko da kuwa akwai matatun man fetur shi ne, babu wanda zai kashe dubban miliyoyin kuɗi ya gina matatun mai domin sadaka ko taimakawa al’umma, yace duk wanda ya gina matatun mai yana yi ne kawai don samun riba.