Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano, Alh. Abba El-Mustapha ya jaddda aniyar hukumar ta kawo tsafta tare da gyara a bangaren masu tallan magungunan gargajiya duba da yadda wasun su ke yada kalaman batsa da hotunan da basu dace ba da nufin tallata magungunan su dan su ja hankalin masu saya.
Shugaban hukumar tace fina-finan ya bayyana hakan ne a harabar hukumar tace Fina-finan ta jihar Kano, jim kadan bayan kammala aikin kaman masu tallan maganin gargajiyar da aka samu da laifin sabawa dokar hukumar a wani aikin hadin gwiwa data gudanar tsakanin jami’an yan sanda da ma’aikatan hukumar tace Fina-finan ta Jahar Kano.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar tace fina-fina Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, yace Alh. El-Mustapha yace doka ce tabawa hukumar damar gudanar da wannan aiki a don haka hukumar zata yiwa dokar biyayya sau da kafa domin cimma nasarar da tasa a gaba.