Gwamnatin Ogun Za Ta Hukunta Masu Zubar Da Shara Ba Bisa Ka’ida Ba

Gwamnatin jihar Ogun ta ce daga yanzu za ta fara hukunta duk wanda aka samu da laifin zubar da shara a wuraren da ba a amince ba, inda hukuncin zai kasance tarar har zuwa Naira miliyan biyu (N2m) ko kuma watanni uku a gidan yari.

Mai ba wa Gwamna shawara kan kula da shara, Abayomi Hunye, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce duk da gargadi da gwamnati ta yi sau da dama, mazauna jihar sun ci gaba da watsar da shara a ko’ina ba tare da bin ka’ida ba.

Ya ce cikin ‘yan makonnin nan an kara samun yawaitar zubar da shara a kasuwanni, lamarin da ke haddasa toshewar magudanan ruwa, gurbatar muhalli, da barazana ga lafiyar jama’a.

“Wasu sun dauki zubar da shara a ko’ina tamkar dabi’a ce. Wannan mummunar hali yana jefa lafiyar al’umma cikin hadari, kuma gwamnati ba za ta kara yarda da shi ba,” in ji Hunye.

Ya bayyana cewa dokar hukumar kula da shara ta jihar Ogun ta 2020 ta tanadi tarar farko ta N25,000, amma idan kotu ta tabbatar da laifi, tarar na iya kaiwa N2m, ko kuma hukuncin watanni uku a gidan yari, ko ma dukkan biyun.

Hunye ya ce gwamnati ta riga ta samar da kwantena na shara a manyan kasuwanni, kuma za ta tsaurara doka domin tabbatar da cewa jama’a suna bin ka’idojin tsaftar muhalli.

Post masu alaƙa

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe