Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5

Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna ta shekaru biyar (MoU) don karfafa hadin gwiwar tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Yarjejeniyar, wacce aka sanar a ranar Talata a cikin wata sanarwa da Ahmed Dan Wudil, Mataimaki na Musamman kan Yada Labarai ga karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya fitar, ta bayyana cewa, hadin gwiwar ta shafi dabarun horar da sojoji, raba bayanan sirri, samar da tsaro, da ayyukan hadin gwiwa.

An sanya hannu a yarjejeniyar ne a Riyadh ta hannun Ministan Tsaro na Nijeriya, Matawalle, da Dr. Khaleed H. Al-Biyari na Saudiyya, ana sa ran yarjejeniyar za ta zama tsarin ci gaban tsaro mai dorewa a fadin kasashen biyu.

Post masu alaƙa

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka