Gwamnonin Arewa za su kafa gidauniyar yaƙi da matsalar tsaro a yankin

Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya sun amince da kafa wata gidauniya domin samar da kuɗin yaƙi da matsalar tsaron da ke addabar yankin.

Cikin sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar, sun ce sun amince kowace jiha ta bayar da naira biliyan ɗaya cikin asusun.

Sai dai gwamnonin ba su yi cikakken bayanin yadda za su riƙa kashe kuɗin.

Dama dai masana tsaro sun jima suna bayar da shawarar aiki tare tsakanin duka jihohin arewa domin magance matsalar tsaron da yankin ke fuskanta.

Yankin arewacin Najeriya ya jima yana fama da matsalar tsaro, inda ƴanbindiga ke kai hare-hare kan fafaren hula tare da garkuwa da su ko kashe su.

haka zalika kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta sake nanata buƙatar kafa ƴansandan jihohi domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.

Cikin sanarwar bayan taro da ƙungiyar ta fitar bayan kammala taron da ta gudanar a Kaduna, gwamnonin sun yi kira ga majalisar dokokin Najeriya da na jihohi su ɗauki matakan tabbatar da hakan.

Matakin gwamnonin na zuwa ne kwanaki bayan da Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ƴansanda domin magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta.

Cikin wata sanarwa da Shugaba Tinubu ya fitar a makon da ya gabata ya ce zai duba yiwuwar amincewa da kafa ƴansandan jihohin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *