Hadejia ta cika shekaru 120 da cin nasara kan turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Tsohuwar birnin Hadejia na shirin gudanar da wani babban taron tunawa da cika shekaru 120 da turjiyar da ta yi wa turawan mulkin mallaka na Birtaniya, inda masu ruwa da tsaki suka jaddada muhimmancin kare al’adu da tarihin gargajiya domin amfanin al’umma ta gaba.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Alhaji Usman Abdul Aziz Galadima na Hadejia, ya bayyana taron a matsayin wani lokaci na zurfin tunani da alfahari ga al’ummar masarautar.
Ya ce bikin, wanda Sarkin Hadejia, Alhaji Dakta Adamu Abubakar Maje Haruna zai karɓi bakunci, zai girmama jarumtakar mutanen Hadejia da suka yi turjiya ga turawan mulkin mallaka a shekarar 1906.
Galadima ya bayyana cewa Hadejia ta tsaya tsayin daka karkashin jagorancin Sarkin Muhammadu Mai-Shahada, inda ta ƙi miƙa wuya ga turawan Birtaniya.
A cewarsa, yaƙin ya kasance mai tsanani, inda sama da mayaƙan Hadejia 800 suka rasa rayukansu, ciki har da Sarkin, yayin da shima kwamandan turawan, Captain H.C.B. Phillips, ya mutu a rikicin.
“Wannan ba kawai yaƙi ba ne, wani muhimmin lamari ne da ya nuna jarumta, sadaukarwa da mutunci wanda har yanzu yake tasiri ga martabar mu,” in ji shi.
Taron na kwanaki biyu, wanda za a gudanar a ranar 24 da 25 ga Afrilu, 2026, zai haɗa da addu’o’i ga jaruman da suka rasu, ƙaddamar da gidan kayan tarihi, ziyartar muhimman wurare, da kuma gagarumin bikin Durbar

Post masu alaƙa

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur

‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz