Hukumar tsaron Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar Lagos ta ce ta rufe wani gida da ake zargin ana amfani da shi wajen safarar jarirai a yankin Badagry, tare da ceto mutane 28 da kuma kama mutane biyu da ake zarginsu kan lamarin.
NSCDC ta ce ta kai simamen ne bayan ɗaukar dogon lokaci tana gudanar bincike da tattara bayanan sirri, wanda ya kai jami’ansu zuwa gidan dake yankin a Okuju, Ilado a jihar Legos.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata masu juna biyu 17 sai yara ƙanana da manya 11.
Kakakin hukumar na ƙasa,Babawale Afolabi, ya ce ana yaudarar mata ne ta hanyar intanet, inda ake musu alƙawarin kuɗi bayan sun haifi jariran.
Hukumar ta ƙara da cewa, an tsare matan cikin mummunan yanayi a wuri mara tsafta, inda ɗaya daga cikin matan ta yi ɓari saboda rashin kulawa.
A ƙarshe NSCDC ta ce an miƙa waɗanda ake zargin da kuma waɗanda aka ceto ga hukumar NAPTIP domin ci gaba da bincike.