Home » Jami’ar Bayero Ta Yaye Sababbin Likitoci

Jami’ar Bayero Ta Yaye Sababbin Likitoci

by Halima Djimrao
0 comment

A wannan makon ne Jami’ar Bayero ta Kano ta yi bikin yaye daliban da suka kammala karatun koyon aikin likita su 316, a cikinsu akwai likitoci 69 masu  jinya ta hanyar gashi da tausar ƙashi da tsokar jiki,  da ma’aiktan jinya 77, da likitoci 58 masu jinyar cututtukan da ake ganowa da na’urorin ɗaukar hoton sassan jiki,  da likitoci 68 masu fasahar gano cututtuka ta hanyar gwaje-gwaje, sai kuma likitocin ido su 44.

Rahotanni sun ce an yi bikin ne tare da halartar shugaban jami’ar ta BUK Farfesa Sagir Adamu Abbas da kuma Aisha Kuliya Gwarzo shugabar Kwalejin koyar da aikin likita a jami’ar ta Bayero.

Bikin yaye daliban yana da muhimmanci a rayuwar sababbin likitocin saboda daga shi sun shiga aiki ke nan, kuma a lokacin ake ƙara jaddada musu nauyin da ya rataya a wuyansu na tsayawa su yi wa al’ummar Najeriya aiki da zuciya ɗaya.

A nasu ɓangare ɗaliban da aka yaye sun yi godiya ga iyayensu da kuma malamansu saboda yadda suka tallafa musu daga farkon karatunsu har ƙarshe.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?