Hisbah Ta Kama Ummin Mama, Kan Zargin Ta Da Yada Bidiyon Tsaraicin Ta A TikTok

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata Matashiya mai suna Rukayya Ibrahim, wacce akafi sani da Ummin Mama, bisa zargin ta da yaɗa hotunan tsaraicin a dandalin TikTok.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbar na jihar Kano, Dakta Mujahedden Aminudden Abubakar, ne ya tabbatar da kama Matashiyar mazauniyar unguwar Medile a karamar hukumar Kumbotso Kano.

Dokta Mujahidin ya ce kama matashiyar Ummin Mama da suka yi, ya biyo bayan korafe-korafen da suka samu kan yadda ta ke yada tsiraici a shafin Tiktok, wanda hukumar ta ce yin hakan ya saba da shari’ar addinin musulinci da kuma al’ada.

Da ta ke bayyana nadamar ta Matashiyar Ummin Mama, ta tabbatar da cewar tan ɗauki bidiyon tsaraicin nata a baya, sai dai kuma ta ɗauki tsawon lokaci da dai na ɗorawa bisa karɓar shawarar saurayin ta.

Ummain Mama ta ci gaba da cewa, sai dai daga bisani wasu ƴan TikTok, suka rinƙa dawo da bidiyon suna ɗora su a shafukan su domin su samu mabiya, lamarin da yaja hankalin Hukumar Hisbar ya kai kan batun, amma dai ta yi nadama hakan ba za ta sake faruwa ba.

 

Related posts

Yan Sanda Dubu 45,000 Ne Za Su Kula Da Zaben Jihar Anambra

Amurka Ta Soke Bizar Wole Soyinka

Iyalan ’Yan Sandan Da Suka Mutu Akan Aiki Sun Samu Tallafin N31m A Jigawa