Home » Hisbah Ta Kama Wadanda Suka Daurawa Kansu Aure Tare Da Waliyansu.

Hisbah Ta Kama Wadanda Suka Daurawa Kansu Aure Tare Da Waliyansu.

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu samari da mata biyar da ake zargin sun daura aure ba tare da izinin iyayensu ko bin ƙa’idojin shari’a ba, a  karamar hukumar Nasarawa dake jihar.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wasu samari da mata biyar da ake zargin sun daura aure ba tare da izinin iyayensu ko bin ƙa’idojin shari’a ba, a  karamar hukumar Nasarawa dake jihar.

Ana zargi wani mai suna ,Aminu mai shekaru 23, a matsayin wanda ya amince ya auri Sadiya mai shekaru 22, tare da Umar mai shekaru 24 da ya kasance wakilin ango, da Abubakar mai shekaru 23 wanda ya kasance waliyyin amarya, sai kuma Usaina mai shekaru 21 da wasu yan mata da suka kasance shaidar daurin auren.

Rahotanni sun bayyana cewa an daura auren ne kan sadaki na naira dubu goma (10,000), ba tare da amincewar iyaye ko izinin mahukunta ba.

Mukaddashin babban kwamandan Hisba na jihar Dr. Mujaheedden Aminudden Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’ansu sun kama mutanen ne bayan samun rahoto daga mazauna yankin da suka nuna damuwa kan yadda matasan suka gudanar da daurin aure ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya saba wa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin da ke kula da lamurran aure a jihar, tana mai cewa za ta ci gaba da daukar mataki kan duk wanda ya karya tsarin shari’a a fannin aure.

Yanzu haka waɗanda aka kama suna hannun hukumar domin ci gaba da bincike kafin daukar matakin doka.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?