Hukumar Alhazan Najeriya ta ce alhazai 13 ne suka mutu a kasar Saudiyya

Shugaban jami’an likitocin Najeriya mai kula da alhazan ƙasar nan, Dr Usman Galadima ne ya bayyana hakan a daren Lahadi a birnin Makkah yayin taron bibiyar yadda al’amura ke tafiya bayan Arafat.

Sannan ya ce, jimillar mahajjata bakwai ne suka rasu kafin Misha’ir – tafiya daga Mina zuwa Arafat, da komawa Mina – yayin da wasu shida kuma suka rasu a lokacin Misha’ir.

Inda ya ba da shawarar a riƙa yi wa maniyyata cikakken gwajin lafiya kafin tafiya aikin Hajji tare da ba da takardar shaidar cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

Ya ce kamata ya yi a hana tsofaffin alhazai da majinyata marasa lafiya daga zuwa Jamarat (wurin da alhazai ke jifan shaidan).

Ya buƙaci jihohin da ke da motocin ɗaukar marasa lafiya su gabatar da su don aiki tare da jami’an likitocin kula da mahajjata na ƙasa don samun ƙarin haɗin kai a kan lamuran da ke buƙatar gaggawa.

Manema labarai sun ruwaito cewa kwamishinan hukumar alhazai ta ƙasa mai kula da harkokin sufurin jiragen sama, Goni Sanda na cewa za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa gida, daga ranar Talata 4 ga watan Yuli sannan kuma za a kammala ranar 3 ga watan Agusta.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr