A yau ne hukumar Hisba ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Kwamandanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ta gana da ‘Yan TikTok a hedkwatar hukumar da ke Sharaɗa.
An shirya ganawar ne domin a sami kyakkyawar jituwa tsakaninsu da Hukumar Hisba, don ƙara inganta tarbiyyarsu.
A yayin ganawar, Daurawa ya yi wa ‘Yan Tiktok ɗin alƙawuran da suka haɗa da ba su jari da aurar da su, har ma da mayar da wasu daga cikinsu makaranta.
A karshe kuma kwamandan ya raba wa kowannensu Naira 2000 a matsayin kuɗin data da kuma na mota.
Manya ‘Yan rawar TikTok ɗin da dama sun samu halartar taron.