DAGA: ZUBAIDA ABUBAKAR AHMAD
Masana kiwon lafiya sun gano cewa, ‘ya’yan kankana na da amfanin sosai ga lafiyarmu, sai dai da yawan mutane ba su san hakan ba.
‘Ya’yan kankana da mukan furzan a yayin shan kankana suna kushe da sinadarin da ake kira da zinc da magnesium da potassium da iron da makamantansu wadanda ke kara wa garkuwar jikinmu karfi.
Sannan sunadaran na magance matsalar ciwon zuciya da hana ko kamuwa da ciwon suga, har ma da taimaka wa jikinmu wajen daidaita hawan jini.
Sauran nau’o’in gudunmowar da ‘ya’yan kankana ke ba wa lafiyarmu sun hada da: kara mana kuzari da inganta lafiyar kwakwalwa da kara kwarin kashi.
Wannan kadan kenan daga cikin amfanin ya’yan kankana ga lafiyarmu.
Da fatan an ilimantu kuma za a cigaba da hadiyar ‘ya’yan kankana daga yanzu.