Home » Hukumar NDLEA a Kano ta kama wata allura mai bugarwa mai nauyinta kilogiram 2,000

Hukumar NDLEA a Kano ta kama wata allura mai bugarwa mai nauyinta kilogiram 2,000

by Isma'il Sulaiman Sani
0 comment
NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEAreshen jihar Kano ta yi nasarar kama wata allura mai bugarwa, wadda nauyinta ya kai kilogiram 2,000 tare da kama wasu mutane biyu.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da kwamandan hukumar Alhaji Abubakar Idris Ahmad ya aike wa manema labarai.

Hukumar ta samu wannan nasara ce kwanaki ƙalilan bayan kama tulin tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,553 da ɗigo 1.

Yaƙin da hukumar ke yi da safarar miyagun ƙwayoyi na nuna irin rawar da take takawa wajen kare lafiyar jama’a da kuma kare al’umma daga illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta yi kira ga jama’a da su ƙara sanya ido tare da kai mata rahoton ɓatagarin da ke shigo da irin waɗan nan haramtattun kayayyaki.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi