Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifin safarar hodar Iblis zuwa ƙasar Saudiyya.
Rundunar ta yi bayanin ne a cikin wata sanarwa da jami’inta na hulɗa da jama’a SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aike wa kafofin yaɗa labarai.