Hutu Na Je A Landan Ba Asibiti Ba – Akpabio

Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya musanta abin da ya kira raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana fama da rashin lafiya.

Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da asuban ranar Litinin daga birnin Landan, inda wasu sanatoci da hadimansa da wasu magoya bayansa suka tarbe shi.

Da yake jawabi ga manema labarai a filin jirgin, Akpabio ya ce batun rashin lafiyarsa ƙanzon kurege ne mara tushe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“Babu maganar rashin lafiya, lafiyata ƙalau. Na tsaya a Landan ne kawai domin hutu, ba rashin lafiya ba,” in ji shi.

Kafin zuwansa Landan, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisa na ƙasashen duniya da aka yi a Geneva na ƙasar Switzerland daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa 31.

Post masu alaƙa

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano