Amurka Ta Yaba Wa Najeriya Bisa Kama Jagororin Ansaru

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya yaba da kama fitattun shugabannin ƙungiyar Ansaru da jami’an tsaronta suka yi.

A ranar Asabar ne gwamnatin Najeriya ta ce jami’an tsaronta sun kama ƴan ƙungiyar ta Ansaru, waɗanda take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022 har suka tseratar da wasu fursunoni.

A wani rubutu da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce, “muna yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Najeriya da jami’an tsaronta bisa samun nasarar kama shugabannin ƙungiyar Ansaru da ake nema ruwa a jallo, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Bara’a da Mahmud al-Nigeri da aka fi sani da Mallam Mamuda.”

Ofishin ya ƙara da cewa kama mutanen guda biyu, “babbar nasarar ce ga ƙasar a yunƙurinta na yaƙi da ta’addanci.”

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya