Iran ta buɗe mashigar Hormuz ga dukkanin jirage

Gwamnatin Iran ta sanar da buɗe mashigar Hormuz ga dukkan jiragen kasuwanci domin su rika wucewa har zuwa ƙarshen tsagaita wutar da aka cimma.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda ya ce: “A cikin tsarin tsagaita wuta a Lebanon, an ayyana cewa dukkan jiragen kasuwanci za su rika wucewa cikin ‘yanci ta mashigar Hormuz har zuwa ƙarshen wannan tsagaita wuta.”

Ya ƙara da cewa wannan zirga-zirga za ta gudana ne ta wata hanya da aka tsara tun da farko, wadda Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Iran ta sanar.

A wani ɓangaren kuma, kafar labarai ta Axios ta ruwaito jami’an Amurka na cewa ana tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan wani shiri mai shafuka uku domin kawo ƙarshen yaƙin.

Rahoton ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ake tattaunawa a kai shi ne yiwuwar Iran ta miƙa sinadarin uranium ɗinta , a musayar Amurka ta saki dala biliyan 20 na kuɗaɗen Iran da aka daskarar.

Post masu alaƙa

Fashewar Tankar Mai Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 8 a Kamaru

Korea Ta Amince Da Taimakawa Rasha

An Rushe Hukumar Zaɓen Burkina Faso