‘Iran ta buɗe wa wani jirgi wuta a mashigar Hormuz

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta ce dakarun juyin juya halin Iran sun buɗe wa wani jirgin dako wuta a mashigar Hormuz.

Lamarin ya faru ne kimanin mil 23 daga arewa maso gabashin Oman.

UKMTO ta ce ma’aikatan jirgin sun samu kuɓuta daga harin.

A wani labarin na daban, wasu jiragen ruwan ƴan kasuwa biyu sun ce an kai musu hari yayin da suka yi yunƙurin wucewa ta mashigar, kamar yadda wasu majiyoyi uku suka shaida wa kamfanin dillancin labari an Reuters.

Ɗazu ne dai rundunar sojin Iran ta sanar sake rufe mashigar Hormuz kwana guda bayan buɗe ta, saboda zargin Amurka da ci gaba da rufe tasoshin ruwan ƙasar.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.