Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta sanar da kama wani mutum mai suna, Umar Sani mai shekaru 30 ɗauke da alburusai guda 100 masu rai na bindiga ƙirar AK-47 a jihar.

Kakakin rundunar jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar,ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar asabar.

Sanarwa ta ce an kama wanda ake zargin, a ranar 17 ga Afrilu, 2026, a wani shingen bincike da ke yankin Yankara kan iyakar jihar Zamfara da Katsina, bayan samun sahihan bayanan sirri.

Binciken ƴan sandan ya gano alburusan da aka boye cikin tankin man babur ɗinsa yayin da yake dawowa daga birnin tarraya Abuja.

yanzu haka yana hannun ƴan sanda yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ƙarin masu hannu a lamarin.

Post masu alaƙa

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.