Majalisar wakilan Najeriya za ta yi zaman gaggawa ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2024 domin shawo kan masu zanga-zanga.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da manema labarai suka yi ido hudu da ita wadda magatakardan majalisar Dokta Yahaya Danzaria ya sanyawa hannu.
Dokta Yahaya Danzaria ya ce, “Bisa umarnin Kakakin majalisar, Honarabul. Abbas Tajudeen, PhD, ya ce a sanar da ku cewa za a yi zaman majalisa ranar Laraba 31 ga Yuli, 2024.
- APC Ta Zargi Masu Zanga-zanga Da Niyyar Kifar Da Gwamnatin Tinubu
- An Tsaurara Matakai A Iyayakokin Najeriya Saboda Zanga-zanga
“Yana rokon ku, ku yi shirye-shiryen da suka dace don halartar taron, saboda za a tattauna muhimman batutuwa a wannan zama.
A farkon makon da ya gabata Ƴan Majalisar suka tafi hutu har zuwa ranar 17 ga Satumba, 2024.