Isra’ila Ta Halaka Shugaban Hamas Ismail Haniyeh

Shugaban Hamas Ismail Haniyeh

Wata sanarwa daga kasar Iran  na cewa Isra’ila ta halaka shugaban Kungiyar Hamas Ismail Haniyeh mai shekara 62 a gidansa da ke Tehran.

Sanarwar da Hamas ta fitar yau Laraba da safe ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da yake domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.

Haniyeh fitacce ne a fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawam, ya jima yana gwagwarmaya kan kisan ƙare-dangin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Tuni dai Gwamnatin Iran ta bayyana ƙaddamar da bincike kan kisansan, ta ce tana sa ran fitar da sakamakonsa nan ba da jimawa ba.

Hamas ta ce kisan Ismail Haniyeh   babban laifi kuma martanin halaka shi ba zai yi daɗi ba.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.