Iyalan sojojin Najeriya za su rabauta da samun tallafin biliyoyin kudi

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya amince Gwamnatin Tarayya ta biya Naira biliyan 18 ga Asusun  Group Life Assurance  domin raba wa ga iyalan sojojin da suka kwanta dama, wajen kare ƙasar nan.

Sojojin Najeriya da dama sun rasa rayukan su ne a yaƙe-yaƙen kare ƙasar nan daga Boko Haram, ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar bayan neman ɓallewa daga Najeriya, wato IPOB da ke Kudu maso Gabas.

Tinubu ya bayar da wannan albishir ne yayin ƙaddamar da Gidauniyar Tallafa Wa Iyalan Sojojin da Suka Kwanta Dama, a wurin Ranar Tunawa da Mazan Jiya ta 24, a Fadar Shugaban, a Abuja.

Ya ce har yau akwai ɗimbin bashin da ke kan gwamnati  na yi wa waɗannan mazan jiya godiya da sakayya, waɗanda suka sadaukar da kan su wajen tsaron ƙasar nan.

Post masu alaƙa

Gidauniyar “Renewed Hope” Ta Tallafa Wa Gidaje Marasa Galihu 154,412 A Jigawa

Manjo Janar Rabe Abubakar Ya Rasu A Hannun ‘Yan Bindiga