An fitar da sabon farashin ƙwai a Kano

Ƙungiyar masu kiwon kaji a jihar Kano ta sanar da ƙarin farashin kwai sakamakon tashin gwauron zabin da abincin kajin ya yi.

Ƙungiyar ta ce bayan nazari da lissafin da mambobinta suka yi kan yadda suke tafiyar da sana’ar tasu, sun cimma matsayar sanar da sabon farashi inda ta ƙara da cewa abincin kaji mai iganci a yanzu ya haura naira 11,000 a kan ko wanne buhu.

Shugaban ƙungiyar, dakta Usman ya ce idan ba su ƙara farashin ƙwan ba, babu riba.

Ya kuma jadadda cewa sabon farashin shawara ce da suka bai wa junansu, ba umarni ba.

Masu kiwon kajin sun ce babban abin da ake hada abincin kajin da shi, wato masara ta yi tsada, lamarin da ya sa wasu ma tunanin barin sana’ar.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 daga masu garkuwa a Kogi.