Jama’a Sun Taimaka Wa Yan Sanda Kama Wanda Ake Zargi Da Jifan Tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ii

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da cewar al’ummar gari sun taimaka mata wajen kamo Wani matashi mai Nasir Idris, dan Shekaru 35 nazaunin unguwar Kofar Mazugal, bisa zarginsa da jifan tawagar mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi ii, a daidai Yan Mota Kofar Wambai Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu