Jami’an NDLEA Sun Kama Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Kan Kifi

Jami’an Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun kama hodar iblis (cocaine) da aka ɓoye a cikin kawunan busasshen kifi da aka shigo da su daga ƙasashen waje.

Hukumar ta kuma cafke wani babban mamba na wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke jigilar su zuwa ƙasashe daban-daban, musamman zuwa Indiya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai da wayar da kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a Abuja ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa nasarar ta samu ne sakamakon bayanan sirri kan ayyukan ƙungiyar.

A cewarsa, jami’an NDLEA na sashen filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) sun gudanar da wani samame na musamman a yankin Ojo na Jihar Legas ranar Alhamis 19 ga Maris, 2026.

A yayin samamen, an kama shugaban ƙungiyar mai shekaru 36 mai suna Akputa Dickson Ejike tare da buhuna uku manya. Bincike ya nuna cewa buhunan sun ƙunshi fakiti 237 na hodar iblis da aka ɓoye a cikin kawunan busasshen kifi, wanda aka fi sani da “Okporoko”.

Jimillar nauyin hodar iblis ɗin ya kai kilo 5.80, kuma an shirya tura shi zuwa birnin Delhi na ƙasar Indiya.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda