Wakilai daga Jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa sun kai ziyara tashar MUHASA Radio da Talabijin, a wani mataki na ƙoƙarin buɗe sashen koyar da aikin jarida a jami’ar.
Farfesa Mustapha Dan Malam ne ya jagoranci tawagar, inda suka gana da shugabanci da ma’aikatan tashar domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi koyar da aikin jarida da kuma muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i da kafafen yaɗa labarai.
A yayin ziyarar, tawagar ta samu tarba daga Shugabar Tashar MUHASA, Hajiya Aishatu Sule, wadda ta bayyana cewa wannan yunƙuri zai taimaka wajen bunƙasa ilimin aikin jarida da samar da ƙwararrun ’yan jarida.
Ta ce buɗe sashen koyar da aikin jarida zai bai wa ɗalibai damar samun ilimi da ƙwarewar da ake buƙata a fannin yaɗa labarai, tare da haɗa ilimin aji da ƙwarewar aiki a kafafen yaɗa labarai.
A ƙarshen ziyarar, ɓangarorin biyu sun jaddada muhimmancin ci gaba da tuntubar juna da ƙarfafa haɗin gwiwa, musamman wajen samar da horo da gogewa ga ɗalibai, domin bunƙasa ilimin aikin jarida da fannin yaɗa labarai baki ɗaya.