An gabatar da jirage marasa matuƙa na ARCO Worldwide Services Limited domin ƙarfafa aiyukan tsaro a Arewa maso Yammancin Nijeriya.

A yayin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, rundunar yan sandan Najeriya ta buɗe wani babban taron tsaro a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, domin duba ƙalubalen tsaro tare da tattauna hanyoyin da za a bi wajen shawo kansu.

Taron mai taken “Appraising the Security Challenges in the Northwest”, wato duba da tantance ƙalubalen tsaro a Arewa maso Yamma, da aka gudanar tsawon kwanaki biyu.

Babban sufeton yan sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa maso Yamma da hukumomin tsaro da su ƙara haɗin gwiwa wajen yaƙi da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, yaɗuwar makamai da sauran matsalolin tsaro.

Da yake buɗe taron, IGP Disu ya ce babu wata gwamnati ko hukuma da za ta iya magance matsalar tsaro ita kaɗai.

Ya ce akwai buƙatar ƙarfafa musayar bayanan sirri, gudanar da aiyukan haɗin gwiwa tsakanin jihohi da hukumomin tsaro, da kuma inganta tsaron iyakoki domin hana miyagun ƙungiyoyi amfani da iyakokin jihohi wajen aikata laifuka.

IGP Disu ya kuma yi gargaɗi kan nuna bambancin ƙabila ko addini wajen yaƙi da ta’addanci, yana mai jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali wajen ganowa tare da gurfanar da masu aikata laifuka, masu ɗaukar nauyinsu, masu samar musu da makamai da masu taimaka musu, ba tare da la’akari da ƙabilarsu ko addininsu ba.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da jami’an tsaro da kuma al’umma.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Ya kuma bayyana cewa matsalar rashin tsaro zata ragu da kashi 70 cikin 100 idan al’umma suka ƙara bayar da haɗin kai, musamman wajen sanar da jami’an tsaro duk wani abin da taimakawa wajen tabbatar da tsaron.

Shi ma babban bako mai jawabi a wajen taron, tsohon Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya yi kira ga gwamnonin Arewa da su haɗa ƙarfi wajen tunkarar matsalar tsaro.

Babandede ya ce jiha ɗaya ba za ta iya magance matsalar tsaro ita kaɗai ba, sai an samu haɗin gwiwa tsakanin jihohin da ke makwabtaka da juna.

A wani ɓangare na taron, an gabatar da jirage marasa matuƙa, wato drones, daga kamfanin ARCO Worldwide Services Limited, inda aka bayyana yadda fasahar za ta taimaka wajen sa ido, tattara bayanai da sauƙaƙa aiyukan jami’an tsaro.

Taron ya samu halartar Mukaddashin sufeton yan sandan Najeriya, DIG Suleiman Mohammed Abdul, da kwamishinan yan sanda, Sama’ila Magaji.

Haka kuma, Kwamishinonin yan sandan jihohin Arewa maso yamma da suka halarci taron sun haɗa da CP A. M. Bello na Zamfara, CP Ibrahim Adamu Bakori na Kano, CP Rabi’u Muhammad na Kaduna, CP Aliyu Umar Fagge na Katsina, CP Hassan Hayatu Shaffa na Sokoto, CP Umar M. Hadejia na Kebbi, da CP Tijjani Murtala na Jigawa.

Daga cikin sauran manyan baƙin da suka halarci taron akwai tsohon mukaddashin sufeton yan sandan Najeriya, DIG Hafiz Inuwa Rinjim, da tsohon Darakta-Janar na hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi, tare da sarakunan gargajiya, yan siyasa, masana, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Ana sa ran taron zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar jihohin Arewa maso yamma da hukumomin tsaro, tare da samar da sabbin dabaru da za su taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin.

Post masu alaƙa

An karrama Muhammad Babandede, OFR, OCM, da wasu kungiyoyi kan aiyukan jin kai ga marasa galihu.

Malaman KASU kimanin 200 ne suka bar jami’ar – ASUU

Babu shugaban da ya sauya tarihin Najeriya kamar Babangida — Tinubu