Matafiya sun shafe sa’o’i a cunkoson ababen hawa a hanyar Abuja-Kaduna

Matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja sun ce sun shafe sa’o’i a makale saboda wani mummunan cunkoson ababen hawa da aka samu a yankin Katari zuwa Gidan Busa da ke kan babbar hanyar. 

Daya daga cikin matafiyar ya shaida mana a safiyar Asabar cewa daruruwan motoci sun makale na tsawon sa’o’i saboda ramukan da suka lalata hanyar mai matukar muhimmanci.

A cewar, wasu daga cikin motocin “tun karfe 2 na dare suke wurin, saboda cunkoson. Jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) sun zo wurin, amma duk da haka sun kasa shawo kan lamarin.”

Matafiyin ya ce, “Ɗaya daga cikin jami’an da na yi magana da shi ya ce, ramukan da ke kusa da wata gada ne suka jawo matsalar. Motoci na yin hadari a wurin, wanda shi ke hana zirga-zirga yadda ya kamata.

“Jami’in ya ce sun tattauna da kamfanin da ke aikin hanyar, Infiouest Nigeria Limited, kan yin aikin gyaran gaggawa a wannan sashe, amma kamfanin bai yi ba.”

Ya yi kira ga ga gwamnati da ta gaggauta aikin hanyar domin kawo karshen wahalar da matafiya da masu ababen hawa suke fuskanta.

An shafe shekaru takwas ana aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano. Duk da muhimmancin sashen Abuja zuwa Kaduna, aikin bai samu ci gaba sosai ba idan aka kwatanta da bangaren Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano.

Yawan motocin da ke amfani da hanyar, musamman a lokacin bukukuwan Sallah, na haddasa yawan cunkoso, inda a lokacin bikin Sallah na baya-bayan nan wasu matafiya suka yi kwanaki a hanya kafin su isa inda suke.

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin kammala aikin hanyar nan da Nuwamba na wannan shekara

Post masu alaƙa

Muhammad Babandede ya gabatar da muhimman shawarwari kan karfafa tsaron yankin arewa maso yamma

An gabatar da jirage marasa matuƙa na ARCO Worldwide Services Limited domin ƙarfafa aiyukan tsaro a Arewa maso Yammancin Nijeriya.

An karrama Muhammad Babandede, OFR, OCM, da wasu kungiyoyi kan aiyukan jin kai ga marasa galihu.