Shugaba Tinubu ya yi kira ga matasa su daina ɗaga tutar ƙasar Rasha yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki a Najeriya.
Tinubu ya yi gargaɗin cewa kar ƴan ƙasar su bari maƙiya dimokuraɗiyya su yi amfani da su.
Cikin wani jawabi da ya yi da safiyar yau Lahadi, shugaba Tinubu ya yi kira ga matasa su yi haƙuri su koma gidajensu, da sannu za a shawo kan matsalolin ƙasar.
A ranar Asabar ne dai hotuna da bidiyoyin ɗaruruwan matasa ɗauke da tutocin ƙasar Rasha suka mamaye kafafen sada zumunta, inda wasu daga cikin su ke kira ga shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya saka baki kan matsalar Najeriya.
Sai dai a yayin wani jawabi da Tinubu ya yi, ya ce matasan su ƙauracewa irin waɗannan kasashe, domin kuwa maƙiya dimokuraɗiyya ne.
- Mun Ba Gwamnonin Jihohi Sama Da Miliyan Dubu Dari 5 Da 70 Don Tallafawa Mutane-Tinubu
- An Samu Hatsaniya Tsakanin Matasa Da Jami’an Tsaro A Kano
Ya ƙara da cewa an shafe shekaru 25 a na Dimokuraɗiyya a Najeriya cikin kwanciyar hankali da lumana.
Tun ranar Alhamis ne dai ‘yan Najeriya suka shiga zanga-zanga a faɗin ƙasar domin neman sauyi daga halin da suke ciki na matsin tattalin arziki.
Sai dai kuma daga bisani zanga-zangar ta rikiɗe a wasu wuraren ta zama sace-sacen kayan gwamnati da ma kwasar ganima a shagunan ƴan kasuwa.