Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta bai wa gwamnonin jihohin Najeriya 36, fiye da naira miliyan dubu dari 5 da 70 don tallafawa talakawa.
Tinubu ya bayyana cewa suna aiko da sakon tallafi wanda suke saka rai zai isa ga al’umma.
wannan na kunshe a cikin jawabin da shugaban ya yi a safiyar yau Lahadi.
- An Samu Hatsaniya Tsakanin Matasa Da Jami’an Tsaro A Kano
- Zanga-zangar Lumana Ta Yi Ajalin Mutane 14 A Najeriya
A kwanakin baya ma gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa kowace jiha tirela 20 ta shinkafa domin rabawa jama’a, sai dai wasu jihohin sun musanta karbar kayan tallafin.
Wasu na gani matsalolin da kasar ke ciki ba iya laifin gwamnatin tarayya bane, tunda gwamnatocin jihohi a yanxu suna karbar karin kaso arba’in na abin da gwamnatin tarayyar ke basu duk wata a matsayin kudin gudanarwa.