Saurayin wata budurwa mai sana’ar awara ya yi mata wanka da tafasasshen mai da take suya da shi a cikin unguwar Samaru da ke Zaria Jihar Kaduna.
Saurayin mai awarar ya yi mata wanka da tafasasshen mai ne saboda ta buƙaci ya daina cinye awarar da take soyawa.
Matashin dai ya yi wa buduwar tasa mai suna Hussaina wannen rashin imanin ne saboda ta nemi taka masa burki a wurin sana’arta, yayin da lokacin yake tsaka da daukar awarar da take soyawa yana cinyewa.
Bayan saurayin ya yi ta daukar awara yana dangwala yaji yana sanyawa a bakinsa, Hussaina ta yi masa magana cewa ya daina, lamarin da ya kai ga cacar baki a tsakanin masoyan.
Al’ummar dake gurin dai sukayi kokari wajen sulhunta su.
Ashe wannan saurayi bai haƙura ba, labewa ya yi bai tafi ba, daga bisani kafin su ankara ya zo ya dauki kaskon suyan awarar ya zuba mata tafasasshen man a jikinta.
A halin yanzu dai, iyayen Hassana, waɗanda masu karamin karfi ne da suka dogara da sana’ar ta, suna rokon masu ruwa da tsaki su kawo musu dauki domin yi mata magani da kuma kwato mata hakki.