Kalaman Da Wani Limami Ya Furta Kan Dokta Idris Dutsen Tanshi Sun Haifar Da Rudani

Kwamishinan ƴansandan jihar Bauchi a Najeriya, Sani-Omolori Aliyu ya yi kira ga ƴan jihar da su kwantar da hankalinsu kan hargitsin da aka samu a wani masallaicin jihar kan batun marigayi Sheikh Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce, “a ranar 4 ga Afriku ne wasu suka kai ƙarar cewa limamin masallacin Galli da ke Jahun, Ahmad Isa Jaja a cikin hudubarsa ya faɗa wasu kalamai game da Marigayi Malam Abdulaziz Idris da ba su yi wa ɗalibansa daɗi, inda suka taru a masallaci domin nuna rashin daɗinsu.”

Sanarwar ta ce hakan ya sa kwamishinan ƴansandan jihar Sani-Omolori Aliyu, ya tura jami’ai na musamman domin tabbatar da kaucewa tayar da zaune tsaye.

“Da jami’anmu suka isa masallacin, sun samu nasarar tseratar da limamin da fatattakar wadanda suka taru cikin ƙwarewa, sannan kwamishinan ƴansanda ya yi umarni a ƙaddamar da bincike domin gano musabbabin lamarin,” in ji sanarwar.

Post masu alaƙa

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda

‘Talauci ya faɗo daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto