Yadda Mele Kyari Ya Miƙa Shugabancin NNPCL Ga Bayo Ojulari

Daga Abubakar Abdulkadir Kurawa

Sabon Shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPCL Bayo Ojulari ya karbi aiki daga hannun tsohon Shugaban Malam Mele kolo kyari a ofishin kamfanin dake Abuja.

A yayinda yake karbar aiki daga hannun tsohon Shugaban na NNPCL Mele Kyari wato Bayo Ojulari ya yabawa mele kyarin abisa kokarin da yayi wajen kawo sauyi a kamfanin.

A cikin wata sanarwa da Shugaban sashen wayar da kai da hulda da jama’a na Kamfanin NNPC Mr Olufemi Soneye yace , sabon shugaban Bayo Ojulari yace zai dora akan nasarorin da Mele Kyari ya samar a NNPCL domin cigaban kasa.

Anasa jawabin tsohon shugaban NNPC Mele kolo kyari yace kofarsa a bude take domin bada shawarwari dan ciyar da kamfanin gaba.

Ya kuma taya murna ga sabon shugaban tare da yi masa fatan Alkairi.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa