Kotu Ta Dakatar Da Gangamin Magoya Bayan Wike A Bayelsa

Wata babbar kotu a jihar Bayelsa ta dakatar da magoya bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike daga shirya gangamin siyasa da suke shirin yi a jihar.

Kotun ta ce a dakata da gudanar da taron har sai ta saurara tare da yanke hukunci.

Asali dai an shirya gudanar da taron ne a birnin Yenagoa a ranar 12 ga watan Afrilun bana, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Mai shari’a I.A Uzakah ne ya yanke hukuncin mai lamba BYHC/YHC/CV/133/2025, bayan kwamishinan shari’a na jihar Biriyai Dambo ya shigar da ƙara.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Afrilu.

Ana dai ta cacar-baki ne tsakanin gwamnatin jihar Bayelsa da magoya bayan Wike na jihar, inda magoya bayan ministan suka dage kai da fata sai sun shirya taron gangamin, shi kuma gwaman jihar ya ce allambaran ba a jiharsa ba.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai