A Kano, an gurfanar da wani lauyan bogi mai suna Zaharaddin Sani Maidoki a gaban kotun shari’ar Musulunci bisa zargin yaudara da cin amana.
Wanda ake zargin dan asalin jihar Kaduna ne ya bayyana kansa a matsayin lauya da niyyar kare wasu mutane a gaban kotu
Zaharaddin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake zarginsa da su wanda ya hada da yin basaja a matsayin dan jarida daga jihar Kaduna.
Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta daure karkashin jagorancin alkalin kotun, Abdulmuminu Nuhu wanda ya daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan gyaran hali.
Hukuncin da Alkalin kotun ya yanke bai ba da damar biyan kudin tara ba, amma zai biya N20,000.
A yayin yanke wannan hukunci dai, kotun ta yi amfani da dokokin shari’a addinin musulinci ta jihar Kano karkashin sashe na 337 wajen yanke wancan hukunci.