Hukumar kidaya ta kasa reshen jahar kano ta yi taron wayar da kan yan jarida don ilimintar dasu tare tuna musu irin shirye shiryen hukumar tayi a nan jahar Kano na gabatar da aikin kidaya.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan taron, babban kwashinan hukumar na jahar kano ismail sulaiman lawan yace an shirya taron ne don ilinmintar da kungiyoyi da kuma yan jarida irin shirin da hukumar tayi don yin kidayar bana.
hukumar ta kidaya reshen jahar kano ta gabatar da wannan taro ne don kara tuwanatar da yan jarida da kungiyoyi irin shirin da hukumar tayi na tunkarar kidaya da ake san ran za ayi a bana .Baban kwamishinan hukumar ta kidayar jama’a da gidaje na jahar kano isma’il sulaiman lawan yayi karin haske game da maka sudin haka wannan taro.
Kwamishinan yace hukumar ta kidaya a matakin na kasa na shirin ganawa da shugaban kasa bola ahmad tunubu don tattaunawa ranar da za agudanar da wannan kidaya.
Shima a nasa jawabin wakilin gwamanatin Kano Muhammad Danyaro ya ce taron zai taimaka wajen bayyana wa jama’a cewar lallai za a yi wannan kidaya kuma tuni hukumar ta kidaya ta gama shirinta.
Tun a watan mayu na wannan shekara, hukumar tayi shirin gudanar da kidayar to amma sai tsohon shugaban kasa muhammadu buhari ya dage aiikin kidayar har sai a rantsar da sabuwar gwamnati.