Hukumar kwanakwana da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta jahar ta kasa wato NEMA na cigaba da aikin ceto, daya daga cikin gine-ginen da gwamnatin kano ta rushe a jahar.
Shaidun gani da ido sun bayyana wa Muhasa cewa ginin ya rushe ne yayin da wasu matasa ke tsaka da cigaba da hakar karafen rodi da aka yi amfani da su wajen ginin Daula, a lokacin da wani sashe na ginin ya rufta musu , inda nan take wasu matasa biyu suka rasa rayukansu yayin da wasu biyu suka jikkata.
Shi ma kakakin hukumar kashe gobara ta jahar Kano wato Saminu Yusuf ya shaida faruwar lamarin sai dai bai bayyana adadin mutanen da abun ya faru da su ba.
Idan za a iya tunawa wannan gini na daula na daga cikin gine-ginen da gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Abba kabir yusuf ta rushe, inda ta yi zargin an gina su ne ba bisa ka’ida ba.