Hukumar jin Daɗin Alhazai ta jihar Kano ta ce akalla maniyyatan jihar 156 ne za su rasa aikin hajjin bana.
Hakan ya faru ne sakamakon sayar da kujeru fiye da yadda aka ƙayyade da tsoffin jami’an hukumar da sabuwar gwamnatin jihar ta dakatar suka yi.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Darakta Janar na hukumar, Laminu Rabiu ya ce hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta ware wa Kano kujeru 6,144, amma jami’anta sun sayar da ƙarin kujeru 156.
Ya bayyana cewa za a binciki jami’an da suka aikata wannan laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu, bayan kammala aikin Hajji bana.
Daraktan ya kuma yi kira ga waɗanda abin ya shafa da su yi haƙuri, tare da alƙawarta musu cewa za a sanya su a cikin sahun farko a aikin Hajji mai zuwa.
Ya zuwa yanzu Hukumar jin Daɗin Alhazan ta Kano, ta yi jigilar maniyyata 2,558, zuwa ƙasa mai tsarki.