Kotun jihar Kano ta yanke wa wani ‘dan kasar Chaina Frank Geng-Quangrong, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe budurwarsa a jihar Kano.
Kotun ta samu Frank Geng-Quangrong, da laifin kashe budurwarsa mai suna Ummukulsum Sani da ka fi sani da Ummita a watan Satumbar shekara ta 2022 a jihar Kano.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa za a gaggauta yanke masa hukunci idan har ya gaza daukaka kara kan hukuncin da kotun da ke zamanta a jihar Kano ta yi.