Kano Pillars Ta Koma Karshen Teburin Gasar Firimiyar Nijeriya

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sake fuskantar wani mummunan sakamako inda ta koma matsayi na 20, wato ƙarshen teburin gasar Firimiyar Nijeriya ta NPFL.

Wannan koma baya na zuwa ne bayan ta sha kashi a hannun Enyimba United a wasan mako na 11, wanda aka buga a filin wasa na Enyimba International Stadium da ke birnin Aba a Jihar Abia.

Ɗan wasan Enyimba, Bassey John, ne ya fara zura ƙwallo a ragar Pillars a minti na 27, kafin Edidiong ya ƙara ta biyu mintuna kaɗan kafin a tafi hutun rabin lokaci, lamarin da ya nuna ƙarara cewa masu masaukin baƙi sun fi ƙarfin Pillars a wasan.

Sakamakon ya bai wa Enyimba damar hawa zuwa matsayi na 6 a teburin gasar da maki 16 daga wasanni 11, yayin da Sai Masu Gida suka sake komawa matsayi na 20, wato a ƙarshen teburin.

Wannan na nuni da cewa ƙungiyar ta Kano Pillars tana cikin tsaka mai wuya a wannan kakar wasan.

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.