Yan Sandan Legas Sun Ayyana Neman Sowore Ruwa A jallo

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta ayyana ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo. 

Wannan mataki da rundunar ta ɗauka na zuwa ne bayan zargin Sowore da yunƙurin ta da zaune tsaye da kawo hargitsi da sunan zanga-zanga a Jihar Legas.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olorundare Jimoh, ya bayyana cewa tun da fari rundunar ta gargaɗi Sowore kan kada ya jagoranci wata zanga-zanga da aka gudanar kan wani rusau da hukumomi suka gudanar a yankin Oworonshoki na jihar.

Sai dai rundunar ta bayyana cewa Sowore ya yi wa gargaɗin nata kunnen-uwar-shegu, inda ya shirya mutane suka fita tituna domin gudanar da zanga-zanga duk da cewa shi bai halarta ba.

Ana iya tuna cewa dai, Sowore, wanda shi ne jagoran “Take It Back Movement”, ya yi barazanar gudanar da zanga-zanga a makonnin baya domin nuna adawa da rusa gidajen da gwamnati ta yi da sunan shirin sabunta birni a Jihar Legas.

Post masu alaƙa

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 6 a Adamawa