Obama Ya Caccaki Salon Mulkin Trump A Amurka

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya caccaki gwamnatin Donald Trump a taron gaggamin siyasa na yantakarar gwamna a Virginia da New Jersy.

Ya bukaci masu kada kuri’a a zabuka masu zuwa da su yi watsi da abin da ya kira rashin bin doka da sakaci da hauka da ake yi a fadar White House.

Obama ya shaida wa Amurkawa cewa Trump da ‘yan Republicans na son su yi tunani domin wasu tsiraru ne kawai a mulki ke daukar mataki amma kuma a bar ‘yan kasa da wahala.

Mista Obama ya yi jan kunne ga ‘yan Republican kan gazawarsu na taka wa Shugaba Trump burki Obama, ba kasafai yake tsoma baki a harkokin siyasa ba amma har yanzu yana da farin jini a tsakanin ‘yan Democrat.

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.