Sabon Sakataren zartarwar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano, Alhaji Lamin Rabi’u ya kama aiki a yau din nan bayan nada shi da sabon gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi.
Yayin da yake jawabi Sakataren zartarwar ya godewa Allah subhanahu wata’allah bisa yadda ya baiwa gwamnan Kano ikon Mayar da shi hukumar domin sake hidimtawa alhazai bakin Allah.
Lamin Rabi’u ya kuma bada tabbacin zai yi duk mai yiyuwa wajen wajen ganin an sami nasarar gudanar da ibadar aikin hajjin bana, Inda ya bukaci alhazan da su bada hadin kai don kyautata musu tun daga nan Kano har zuwa can kasa mai tsarki.
Rhotanni sun tabbatar da cewa wannan ne karo na uku da Alhaji Lamin Rabi’u ya sake komawa hukumar a matsayin Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano.